TABBATAR ADDINI DAGA BAKIN SHEIK IBRAHIM ZAKZAKY (H). A Shekara ta 1990.

 kashi na (01)

Wani bangare na Jawabin Sayyeed Ibrahim Yaqub El-Zakzaky mai suna : (Tabbatar Addini), wanda yayi a shekara ta 1990 ka nema zaka samu, Jawabin nada Minti 88 da Sakan 47.

Abinda nikeso in tunatar damu shi ne Minene ma'anar wannan kiran, yaya akeyin wannan kira na Harkar Musulunci, Harkar Musulunci ba Kungiya bace ta wasu Mutane, wane matakai akebi a Harkar Musulunci, wadanne matakai za'acimmawa nan gaba domin cimma nasara akan wannan Kiran na adawoma hanyar Allah, minenen nasarar wannan kira, akwai wasu fahimce-fahimce da wasu al'umma keyima wannan kiran na Harkar Musulunci bana dai-dai ba.

Ma'anar Kiran Harkar Musulunci : Wannan kirane na tabbatar da addinin Allah. Allah yayi alkawali ga wadanda sukayi Imani da Aiki na gari zai tabbatar dasu da addininsa zai yarje masu, alokacin da Allah yace zaitabbatar da addininsa lokacin rikon Kasa yana hannun Kafiran Gabas dana Yamma. Wannan Da'awar tabbatar da addinin Allah kamar yadda acikin Alqur'ani yake a rubuce

Aduk lokacinda Addinin Musulci yayi rauni za'asamu wani Bawan Allah yayi kira adawo ma addinin Allah kamar misalin Sheik Usman dan Fodiyo, muma muna kirane da adawo ma addinin Allah yanzu a Kasarnan addinin Allah ake, addinin tabbace yacke a Kasarnan.

Bamuce mukadaine Musulmai ba, Bamuce zamu fidda wani daga Musulunci ba, munshaida da La'ilaha'illah abinda ya ragemana shine aiki da shi, muna kokarin cewa addini shizai tafiyar da rayuwarmu idan har Mutum yanganmu zakaga addini kake kallo, idan ka saurari maganarmu zakaga addinine ke fitowa daga bakinmu damu da addini abi guda ne.

Akwai hanyoyi da dama wadan da mutane ke raya addini Musulunci kamar makarantu da sauransu, munaso mufara da'awa da matakin farko kamar yadda Manzon Allah yafara da'awarsa, zamubisu tiryan-tiryan, daki-daki, daya bayan daya kamar na Manzon Allah. Matakin Harka Musulci guda(4) irin na Manzon Allah.
1)Da'awa (2)Bara'a, daga baya na ukku dana hudu subiyo baya 3)Hijira 4)Nasara.

Al'umma ta dauki rudani dangane da irin wannan al'amarin na Harkar Musulunci sabanin yasha bam-ban da sauran Al'adu, addini yakamata Al'umma tarike ba al'ada ba!, duk da cewa baturo yazo ya cusama al'ummar Kasata irin tasa al'adar harya koyar da wasu cikinmu harsun iya, sai bature ya koma Ingila yayi zamansa, Al'ummarmu na koyar da al'adarsa Bature a Kasar mu anbar addinin Allah.

 Sheik Ibrahim Zakzaky cikin Jawabinsa mai Suna (TABBATAR ADDINI) a shekara ta 1190.

    Muhadu Kashi na (02).

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post