SHIN JAMI'AN TSARON NAJERIYA DAMA KUNA DA DUBARUN KUBUTAR DA MUTANEN DA AKAYI GARKUWA DASU NE, KO KUWA AKWAI BAMBANCI NE A TSAKANIN YAN NAJERIYAR DA AKE KAMAWA??

SHIN JAMI'AN TSARON NAJERIYA DAMA KUNA DA DUBARUN KUBUTAR DA MUTANEN DA AKAYI GARKUWA DASU NE, KO KUWA AKWAI BAMBANCI NE A TSAKANIN YAN NAJERIYAR DA AKE KAMAWA??



✍️Musa Ibrahim Daura, Tare da MSN012


Dazun nan nagama jin rahoton BBC Hausa inda naji ana hira da malam Bala lau shugaban kungiyar izala ta kasa, yana sanar da cewa jami'an tsaron najeriya sun kubutar da Malam Ahmed Suleiman, malamin nan da masu garkuwa suka Kama tare da wasu mutane shidda. Masu garkuwar sun nemi kudi miliyan dari uku, har aka dawo miliyan talatin.

Kamar yadda naji daga bakin malam Bala lau, Cewar an kubutar da malamin ba tare da bada Ko sisin kwaboba, ta hanyar dubaru na jami'an tsaro Wanda bai bayyana suba. Lalle wannan abin yabawa ne da jinjinawa jamai'an tsaron mu.

Ina taya malam murnar kubuta tare da fatan Allah ya kiyaye afkuwar haka anan gaba, yakuma Karawa malam lafiya, ina kuma fatan Allah yakare dukkan sauran Musulmi da kuma mutanen kasar nan daga fadawa irin wannan tarko.

TAMBAYA.

shin dama jami'an tsaron mu suna da kwarewa da iya aikin kubutar da mutane? Ko kuma akwai wadanda sukafi wasu muhimmanci ne a kasar, Domin naga kusan kullum ana Kama bayin Allah marassa galihu, wadanda basu da yadda zasuyi, wasu kuma ayita karaya tare da sayar da dukkan wata kaddara Domin aje a kubutar dasu, Kai! Wasu ma ta wannan hanya suke rasa rayuwar su, wasu kuma a keta musu mutuncinsu, kusan kullum sai an samu matsala irin wannan. Domin ko kwanakin baya haka aka Kama wasu yan biyu tare da yayarsu amma saida aka biya makudan kudade aka sako su.

To miyasa? Minene dalili? Yakamata hukumomi kuji tsoron Allah ku sani wallahi duk ran wani Dan kasar nan yana da muhimmanci kuma yana da hakki akanku, dole ne ku kareshi ko ku kubutar dashi daga mahara Ko Mai rauninsa. Idan kuma kukayi banza dasu sai Allah yayi maku hukunci a kan haka, tun anan duniya kuma kuje lahira ku gamu da Allah.

Zamuso ace kullum irin wannan kokari da kukayi, shine aikin ku domin a zahiri kunyi rantsuwa zaku Kare dukkan yan kasa tare da kare mutuncinsu, to amma sai naga alamar kamar ba haka bane kuna Nema ku maida mutanen kasa akwai ajin farko da kuma aji na biyu. (Wato First Class da second class).

Ina fatan wannan rubutu nawa zai zaburaku tare da farkar daku daga barci idan shi kukeyi idan kuma idon ku biyu to ku dage akan aikin ku.

Musa Ibrahim Daura
27-3-2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post