FILIN MAWAKA:-Hirar da Shafin Ma'asumah Yayi Da Bello Shehu Alkanci Sarkin Wakar Kasar Hausa.


Ko Wannenmu ya kamata yasani tallata fikirar Jagorane aikinsa, ba ra'ayinsa ko na wani ko wasu ba.

________________
Hirar da Shafin Ma'asumah  Yayi da Ficeccen mawaqin nan Kuma Sarkin Mawaka Wato Sidi Bello Shehu Alkanci Talatar Mafara a a Shekarun Baya, Tun Lokacin da Shafin Ma'asumah Yana Ma'asumiyya kafin Chanjin Suna.

Insha Allah zamu Shiga Cikin Hirar kai Tsaye...

.
Ma'asumiyya: Masu sauraronmu zasu so sanin dawa muke tare a wannan lokacin tare da dan takaitaccen tarihinka?
.
Bello Shehu Alkanci: "To da farko sunana Bello Shehu Alkanci Talata-Mafara. Ni Basakkwace ne a asali a unguwar Alkanci ta tsakiyar birnin a da. Amma a Mafara ta jihar Zamfara aka rikeni bayan rasuwar mahaifina. Kuma yanzu haka a ciki nake zaune tare da iyalaina. Shiyassa a cikin sunana dole akwai Mafara.

Nayi karatun firamare a 1985 zuwa 1991. Na kammala sakandire a shekarar 1996. Daga baya naje jami'ar Usmanu Danfodiyo nayi digiri a sashen nazarin harsunan Nijeriya a matakin digiri na farko wato (B.A. Hausa)duka a cikin garin Sakkwato."
.
Ma'asumiuya: A kalla yanzu kakai shekaru nawa da fara waqa kuma yaushe abun ya fara gudana, kuma me yaja hankalinka har ka fara gudanar da waqoqin Manzo da Ahalul-bait (as)?
.
Bello Shehu Alkanci: To a gaskiya ba waken harka na fara ba. Ina wakoki tun gabanin in fahimci harka tun ina karamin Dan sakandire. Alhamdulillah wakokin da nake yi a lokacin na fadakarwa ne da gargadi kamar yadda naji mahaifina yana yi. Kuma ana yawan sanya shi a Rima radiyo Sakkwato. A takaice na fara rubuta waka a 1991 lokacin hadarin jirgin saman alhazan Nijeriya. Daga baya an shirya gasa a makarantarmu na wakoki. Nazo na daya 1994. Amma na fara wakokin harka ne a shekarar 1995. Bayan fitina tawayiya. Amma kafin nan ina kawai sauraren mawakan harka ne a lokacin. Abinda ya ja hankalina kuwa karfafawa ce ta wasu 'yan uwa da suka San ina waka. Sai suka karfafani in fara wakokin gwagwarmaya. Ganin tasiri da karbuwar abin yasa muka dage har zuwa yau."

Danna Bottom dinnan domin yin Download din daya daga cikin sanannun wakokinsa

.
Ma'asumiyya: Zamu iya cewa Malam, Malamine a waqa musamman kasancewarka masani a bangaren yarerruka na kasar nan kuma mazauni a yankin mawaqan hausa, Shin yaye kuke ganin yanayin waqoqinmu na zamanin yanzu dana da na baya?
.
Bello Shehu Alkanci: To ina dai iya amsa sunan dalibin nazarin waka. Sannan ban fahimci hakikanin tambayarka ba cewa wakokinku na zamani da na baya. Saboda su masana dai sun raba wakokin Hausa gida biyu; wato wakokin baka da suka kumshi irin na makadan Hausa irin su Shata da Dankwairo da Narambada da sauransu. Da kuma rubutattun wakoki wadanda suka kumshi wakoki na madahu da fadakarwa da wa'azantarwa da sauransu wadanda suka tafi akan tsari da kafiya da awo irin na wakokin Larabawa. Wadanda da mafiyan jigoginsu na addini ne. To ka ga yanzu an samu cigaba maiyawa da fadaduwa a fannin waka tun daga karni na 18 zuwa yau. To ban sani ba kana nufin bambancin wakokinmu da na makadan gargajiya ne? Koko kana nufin bambancin rubutattun wakokinmu na yanzu da zamanin da irin zamanin su Shaihu bin Fodiye (T).?
.
Ma'asumiyya: Eee yanayin Waqoqinmu na yanzu, ko nace irin fasahar mawaqan yanzu da ake amfani da na'urori na zamani, da irin waqoqin da kamar irin na zamanin shehu Usman bin Fidiyo da ake yinsu a rubuce, shin wanne irin bambancine aka samu ko canjan yanayi da waqoqin wancan zamanin dana yanzu?
.
Bello Shehu Alkanci: "To dukanmu dai ana kiran wakokinmu rubutattun wakoki. Saboda sigoginsu da tsarinsu yazo ne bayan Hausawa sun samu ilmin Larabci suka iya kwaikwayi salon zubi da kafiya na Larabawa. Amma yanzu wasu rubutattun wakokin jigonsu da salonsu bai da bambanci da na Mawakan baka.

Sannan a takaice an samu cigaba daga wancan zamani da yanzu ta fuskacin yawa da fadada da shigo da wasu sababbin jigogi na waka. Amma bambancin da na iya fahimta tsakani shi ne su akasarin marubuta wakokin da Malamai ne masana ilimin aruli da sauransu. Sukan dora wskokinsu akan wannan ta yadda ko baka taba jinta ba idan ka ganta a rubuce ko a kasuwa ne zaka iya dauka ka kirkira mata sauti ka rera. Amma mafiyawan marubuta wakokin yanzu wakokinsu ba su karantuwa in ba sun karanta maka kaji sautin ba. Saboda ba mu da kwarewa na ilimin aruli da fasaha irin tasu. Za ka ga mun fi muhimmantar da rangaji da kidan wakar. Wani lokaci idan ina karanta wakokin irinsu Malam Akilu Aliyu da Umarun Nasarawa da sauransu na kan jinjina musu hada baiti mai ma'ana da kafiya da fasaha. Amma dai alhamdulillah muma wasu mawaka a zamaninmu suna fitar damu kunya a fagen fasaha da balaga din."
.
Ma'asumiyya: Idan muka dawo cikin ita harka din kasan tuwarku wasu jigajigai a cikin wannan harka ta bangaren Ittihadu, Koma nace ita wannan ittuhadu tana gudanane bisa kokarinku   zamu so musan yaushene kuka fara gudanar da wadannan aiyuka din?
.
Bello Shehu Alkanci: To dama dai اذاكنت في امرفكن فيه . Al'amarin ittihadus shu'ara tun sadda aka samar da ita muke cikinta kuma muke bada gudummawarmu a ciki tun daga matakin garuruwanmu da yankunanmu har zuwa fadin kasarnan bakidaya."
.
Ma'asumiyya: Kusan zamu iya cewa Al'amuran Uttihadu kullum kara fadada suke musamman bayan waqi'ar nan dubi da yawan tarurrukan da ita kanta ittihadun take gudanarwa Shin minene ya zaburar daku ga hakan?
.
Bello Shehu Alkanci: "A'a dama kafin waki'ar nan Ittihadu ta farfado game da wasu matsaloli da suka so yi mata tarnaki a baya. To kasantuwar sa bakin Jagora (H) sai suka kuranye. Don haka koda waki'a tazo an fara gudanar da mu'utamar babba a Zariya da kuma Majlisoshi na Munasabobi wanda Su Sayyid (h) kan yi sanarwa da kansa kuma su zo su zauna suna sauraren Mawaka. To wannan ya dada bamu courage. Kuma mun ziyarceshi kusan na karshe kafin waki'a muka yi tambayoyi ya ba mu amsoshi. A cikin maganganunsa masu albarka yake cewa:
"Ya san wakoki sun taka rawa a marhaloli dabam-dabam a cikin harkarnan, tun a farko-farko ya zuwa lokacin tawayiya da lokacin waki'ar Abaca. Yace kuma wakoki sun taka rawa wurin Istibsar  na al'amarin Ahlulbait (as ). To shi ne a karshe yake cewa ga wani aiki da rage muku shi ne wayar da kan sauran al'umma al'amarin sauran A'imma  (as). A takaice dai wannan shine sirrin abinda ya zaburantar da mu wurin cigaba da gudanar da al'amarin ittihadu a garuruwa da yankuna a da'irori dabam-dabam."
.
Ma'asumiya:Wasu sunata yayada cewa tsakaninku da Uzairu Badamasi babu ga maciji shin minene gaskiyar lamarin


Bello Shehu Alkanci: (dariya)  A'a ba haka bane ba mu da wani rashin jituwa da Uzairu. Amma na san dalilin wakar Dansandan ciki na bodinga ne ake ganin haka.

Wato abinda ya faru matsalace ta gayyata da wakilin 'yanuwa na Bodinga ya sanya ni in gayyato musu Uzairu. To bayan munyi waya ya karbi gayyatar ya sanya musu rana. Na sa suka tura masa kudi a akawun. Da ranar tayi sai bai zo ba kuma bai aiko uzuri ba. Na nemeshi a waya baya dauka a karshe sai ya kashe wayar. Na shiga damuwa sosai kasantuwar suna shauqin zuwansa. Ni kuma sun sa ni in nemo musu shi saboda sanin alakar da ke tsakanin mawaka ta sanayya da mutunta juna. Labari ne mai tsawo. Amma a karshe sai wani da muke tare dashi wanda yasan yadda aka kitsa gayyatar kuma a gabansu nake yawan yin waya da uzairu don kar ya manta. To shi dan uwan ne ya fusata ya kira Uzairu ya gaggaya masa maganganu masu zafi a matsayin 'yanbodinga. To sai Uzairu ya kauda kai ga kuskuren da yayi ma yanbodinga sai ya maida akalar gayyatar a matsayin jami'an tsaro ne suka shirya masa tarko. Yayi waka ya sake ta cikin yanuwa har ana masa sambarka. To ganin haka sai naga ya zama wajibi ayi martani tare da warware shubhar da ke ciki da kuma bayyana hakikanin duk abinda ya faru. Wannan ya jawo cece-kuce a social media da sauran yan uwa. Alhamdulillah ina tunawa manyan 'yanuwa sun kirani daga wurare dabam dabam. Shahid Malam Kasim ma ya kirani har ya bamu shawarwarin yadda za a warware matsalar. Duk wannan bayanan abinda ya faru suna can cikin wakar da mukayi da ta shi Uzairun. Bai dace ayi ta maimaitawa ba tunda ya wuce. Ko yanzu saboda imma tambayar adalci ne na fada muku. Sannan ko ban fadi ba tarihi zai fadi tunda lamarin ya riga ya auku kuma anyi wakokin tarihi ya shajjala. Don ko wata biyu da suka shige wani mai Malami mai karatun digiri na uku (Phd) ya zo gida ya same ni a cikin abinda yake bukata har da wadannan wakoki da mukayi tsakaninmu da uzairu. Saboda wani karatu ne ga masu nazarin adabin waka.

To amma dai in gaya muku gaskiya a yanzu bamu da wata matsala da Uzairu Badamasi. Ko bayan wannan mukan hadu a wurin taruka da wurin shiga mota. Mu tsaya mu gaisa cikin nishadi da raha. Dama kafin nan mukan hadu a wani garin muyi majlisi tare mu kwana wuri daya daki daya. Don haka babu zancen babu ga maciji (murmushi).
.
Ma'asumiyya: Wacce siffa ko tsari ya kamata ace mawaqin Harka Islamiyya ya siffantu dashi a dabi'unsa, mu'amalarsa da kuma yannayin da ya kamata ace waqarsa ta dauru a kai?
.
Bello Shehu Alkanci: "To dama dai a wurin mu'utamar da ittihadu me shiryawa su Malam (H) sun sha kira ga mawaka su zama masu kyakkyawan dabi'u musamman har yake cewa saboda shi mawaki yana da tasirin da har masoyansa sukan kwaikwayi hatta sa suturarsa imma yana wata dabi'a kamar tara suma to masoyansa irin nasa zasu kwaikwaya. Ya bamu misali da mawakan jahiliyya irinsu Bobmali. To kaga yana da kyau mawakin harka ya siffantu da dabi'u masu kyau kamar amana da cika alkawari hatta a gayyatar da 'yanuwa suke masa a garuruwa. Duk Malam sun gaya mana har da korafin da suke ji game da wasu mawakan ya kan gaya mana. Don haka ni abinda zan cewa mawaka su rika neman abinda Jagora ya fada game da su domin su kokarin kiyayewa.

Ta bangaren waka kuwa, ina kira ga Mawaka da mu kara inganta fasahar wakokinmu da salon isar da su ga al'umma. Ta yadda kowa zai iya saurare ba sai Dan harka ba."
.
Ma'asumiya: Wani mai Suna SANI YUSUF ya turo mana Tambaya ta E-mail dinmu Mdanmasaniskff@gmail.com yake cewa:- Ma'asumiya Slam ga tambayata ga bello Shehu Alkanci idan mutum yana so ya gayyace ka Bikin aure a gidan sa ko suna wacce hanya zai? Allah ya kwato mana abba (h).
.
.

Bello Shehu Alkanci:Gayyatata ba ta bambanta da sauran yadda ake gayyatar kowane mawaki ba. Wato na san masu gayyata sukan nemi lambar Mawaki ne ko same shi in ana kusa su sanar dashi programme dinsu. Su gaya masa rana ko ya basu rana in yana da sukunin zuwa zai karba musu. Su ba shi kudin mota kamar yadda aka saba. Na san ina karba gayyatar 'Yan uwa da da'irori tun lokacin ba wayar hannu. A lokacin akan rubuto takarda ne a turo ko a aiko wani Danuwa ga Mawaki. Na san an taba gayyatata a Legas bikin wasu 'yan uwa amma a lokacin ba wayar salula to masu bikin sun turo wani Dan uwa ne takanas tun daga Legas har gidana ya sameni.
.
Ma'asumiya: Tambayar da take yawo acikin Zukatan yan uwa dama jama'ar gari itace miye dalilin da yasa ake kiranka sidi Shin kana daga cikin Shurafa ne ko kuwa?

.
Bello Shehu Alkanci: Eh, Lalle a zuriyarmu muna da salsala (shajara) a rubuce wanda kakanninmu suka ajiye mana wanda take dauke da jerin sunayen kakanninmu tun daga wani da ake kira Sidi Maigari har zuwa Imam Hassan Almujtaba zuwa ga Sayyidina Ali (as). Na san da wannan salsala tun ban fahimci mazhabin Ahlulbaiti ba. Da sauran bayanai masu tsawo. Na taba bincike tun sama da shekaru sha bakwai ga wani Dan uwa Malami ne yayi min bahasi game da tarihin Imam Hasan da zuriyarsa wadanda suka wanzu bayan karbala har zuwa Afrika. To daganan na samu sunan daya daga sunan jerin kakanninmu wanda yake a jikin salsalar. Kuma a lokacin ban gayawa shi Dan uwan sunan kakan namu ba don gudun kar in sami shakku, wannan shiyasa wasu yan uwa suke kirana da wannan sunan.

.

Ma'sumiyya: Ko akwai wani karin bayani ko wani saqo mai muhimmanci da zaka so ace masu sauraro sun sani daga gareka wanda bamu tambaya ba?
.
Bello Shehu Alkanci: To bayani ko kirana ga Mawaka 'yanuwana shine cewa, mu yi kokari a dukkan wakokinmu na harka su zama daidai da fikirar da jagoranmu ya dora mune. Kamar yadda ya bukaci muyi hakan a wani taro da mukayi ya rufe mana. Wato kowanenmu ya kamata ya sani tallata fikirar Jagora ne aikinshi ba tallata ra'ayinshi ko tallata ra'ayin wani ko wasu ba. Sannan mu yi kokari mu kwakkwafa matsaloli idan sun taso ba mu karfafasu ba. Wannan ma Malam (h) ya umarcemu da haka. Har yake cewa shi mawaki yana iya maida karamin al'amari babba. Don haka yace mu rika tafiya da harka kunnen doki. Sannan mu rika halartar tarukan da ittihadu take shiryawa saboda jagoranmu ya nuna jin dadinsa da haduwarmu har ma yana karfafarmu akan haka.
Don saudayawa wasu mawakan saboda rashin halartar tarukan irin wannan zaka ji sunyi waka tayi ma'ana amma a ciki sai zuba shirme da rashin saiti kasantuwar basu da masaniya ya Jagora ya tsawatar ko ya nuna yadda ya dace?
Haka kuma janibin matasan mawakanmu musamman masu kama hip hop din nan musamman suyi kokari su zama sun bambanta da na Jahiliyya din a aiki da siffa. Don kar ya zama wurin gyaran doro a karya wuya. Duk wadannan su Malam sun mana magana a wurin mu'utamar dinmu na Ittihadu.

Haka kuma dukka bangarorin masu bada gudummawa a waka ta bangaren hurras ne ko matasa a wurin slogan na muzahara da wakokin jaje duk mu San muna wakiltar harka da fasaharmu ne a cikin al'ummar nan da Sayyid ya ke kira ta samu tsira.
.
Ma'asumiyya: Mun gode da lokacinka da ka bamu Allah ya kara hasken zuciya da ruhi.
.
Bello Shehu Alkanci: Ilahi ajib, nima na gode muku masu shafin ma'asumiyya.

Allah Ya saka muku da alhairi.
.
Daga Ma'asumiyya Nigerian News 🌎
Tare da Wakilinmu
Salisu Umar Mazaje
09021381323


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post