Ⓜ-----daya daga cikin mambobin majalisar wakilan Najeriya, Chika Adamu, ya yi zargin cewa, kisan tsohon shugaban hafsin dakarun tsaro na sojin Najeriya, Air Chief Marshal Alex Badeh, wata kitimurmura ce da aka kitsa ta.
Adamu mai wakilcin shiyyar jihar Neja a karkashin inuwa ta jam'iyyar mai mulki ta APC, ya bayar da shaidar hakan ne cikin zauren majalisar wakilai yayin zaman da ta gudanar a jiya Alhamis.
Dan Majalisar ya ce, kisan tsohon shugaban hafsin dakarun sojin Najeriya babban rashi ne ga al'ummar jihar Adamawa da kuma kasa baki daya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, furucin Adamu ya biyo bayan cecekucen da ya haure ne a zauren majalisar dangane da yiwa lamarin tir gami da Allah wadai.
Ya kuma bayyana damuwarsa gami da fargaba dangane da yadda kashe-kashe da zubar da jinin al'umma ya zamto ruwan dare sakamakon rashin ingataccen tsaro a fadin kasar nan.
Cikin nasa jawaban, Toby Okechukwu, dan majalisa mai wakilcin shiyyar Enugu a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, ya zargi hukumomin tsaro dangane da tabarbarewar al'amurra a cikin kasar nan.
______________________
Ma'asumiya Nigerian News Update;
Wakilinmu;
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST
Tags:
Labaran Duniya
