KUNGIYOYIN PALASDINAWA [Palestien] TA HAMAS DA KUNGIYAR JIHADUL AKBAR SUNYI ALLAH WADAI DA RUSHE GIDAJEN YAN GWAGWARMAYA DA HARAM TACCIYAR KASAR ISRA'ILA KEYI,



Ⓜ--------Mai magana da yawun kungiyar gwagwarmayar musulunci Hamas rushe gidajen 'yan gwgawarmaya da kuma yi musu barazanar kora,
yana nuni da yadda haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci kasa ne a agaban al'ummar palasdinu
Abdullatif al-qanui ya kara da cewa; Rushe gidajen da 'yan Sahayoniya suke yi ba zai hana samarin yankin yammacin kogin Jordan yi gwagwarmaya ba, kamar yadda barazanar da 'yan sahayoniyar suke yi wa iyalan 'yan gwagwarmaya ba za ta raunana su ba.
Ita ma kungiyar Jihadul Islami ta yi tir da rushe gidajen 'yan gwgawarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ilan take yi tare da cewa babu inda zai kai haramtacciyar kasar Isra'ila,

Piraministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamine Natenyahu ya ba da umarnin rushe gidajen iyalan Palasdinawan da su ka kai hare-haren daukar fansa akan 'yan Sahayoniya.
   _____________________
Ma-asumiya Nigerian News Update,
Wakilinmu;
        👇🏽
 Mahadi Tukur Almizan,
DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post