Farfesa Ango abdullahi Yabayyana dalilin kungiyar dattawan arewa na janye goyon bayanta na sake zabar buhari a 2019




Kungiyar dattawan arewa dai tasha suka bayan da ta sanarda janye goyon bayanta na sake zabar buhari akaro nabiyu,

Anji wannan matakina kungiyar ta dattawan arewa ne daga bakin Farfesa Ango Abdullahi, hakan nema yasa masu yin suka gameda da wannan mataki, suka yita surutai akanshi Abdullahin,

Sedai Farfesa Ango Abdullahin yashaidawa manena labarai dalilansu na daukar wannan mataki, ta wayar tarho.


Hirar Ango Abdullahi Ta Wayar Tarho Kan Dalilinsu Na Kin Zabar Buhari A 2019
Na bugawa Farfesa Angon Abdullahi waya da tambayar me zai sa a matsayinsu na dattawan Arewa su ce kar a zabi Buhari bayan su suka ce a kori Goodluck a zabi Buhari, sai ya ce:
Tukur, ya kamata ka gane ba mutum muke goyon baya ba. Mutuncin jama'armu da cigabansu muke nema. Wanda zai kare mana hakkinmu kuma ya kawo mana cigaba shi ne abin a zaba. Mun kori Goodluck saboda sakaci a kan Boko Haram da zaluntarmu wajen rabon arzikin kasa. Yanzu bamuga canji ba. Boko Haranlm suna nan domin Buhari yana sakaci baya iya hukunta jamian soja da suka gaza. Haka ne?
Sai na amsa.Ina ji, Yallabai.
Yauwa. Yau an shiga shekara ta hudu a mulkin Buhari anyi kasafin kudi yafi tiriliyan 35. An kashe samada da tiriliyan 17 a aiyukan raya kasa. Yaro, kasan nawa aka kashewa Arewa?
Allah kadai masani, Yallabai, na amsa.
Gaba daya ba a kashewa Arewa tiriliyan daya ba. Komai wannan bawan Allah yakai can Kudu. Talauta mutanen Arewa yake so yayi koko baisan maanar yin hakan bane? Ina amfanin zaben nasa? Koko sai ya gama tsiyatamu ya zo yana cewa Arewa fatara da rashin zaman lafiya ya yi yawa. Comrade!
Na ce , na'am.
Kana jina.
Ina ji, Yallabai.
An ce ana sallah don lada ne.
Shi ma mun zabe shi ne don Arewa ta sami lada. Idan ya raya kudu mu kuma an barmu a baya , ina amfaninsa a garemu da yayan mu nan gaba?

 Ku ne shuwagabani a yanzu.
 Mu tamu ta zo karshe, Tafiya lahira ya rage mana.
Allah ya gyara?

Kasan mun yi magana dashi sau dayawa, amma ya kasa komai.
Da alamu tsoronsu yake.

 Yana ganin idan bai nuna musu baya son nashiba za su koreshi. Ga shi babu abinda za ka gayamai ya fahimta.

Ko titin jirgin kasa da ya yi wa Legas ya shafe kudin da ya kashewa Arewa baki daya banda tituna da sauran projects da yayi a Legas. Babu Alamun zai canza don ya yi mana adalci, Ko kana ganin da wata mafita, yaro?

Abin sai addua, Ranka ya dade.
( da sauran maganganu)
YA KAMATA BUHARI YA SOMU KAMAR YADDA MUKE SONSHI. KAR YA BARI DUNIYA TA YI MANA DARIYA.

      ____________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update;
Wakilinmu;
      👇🏽
Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post