Ⓜ__An gano zunzurutun kudin takalman da Shugaba Buhari ke sawa

INDARANKA!!!

Ⓜ__An gano zunzurutun kudin takalman da Shugaba Buhari ke sawa





Wasu 'yan sa ido a Najeriya sun yi binciken kwakwaf inda kuma har suka gano ainihin kudin takalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya ke sanyawa musamman ma a cewar su lokacin da kasar ke fama da tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Kamar yadda muka samu, wata kafar yada labarai ta zamani ta yi ikirarin cewa takalman na shugaban kasar Samfurin kamfanin Gucci ne kuma ana sai da su akan kudin Amurka $640 wanda yayi daidai da N223,905 akan canjin $1 a N345.

Jam'a da dama dai nata cecekuce akan wannan Al'amarin.
Wasu na ganin kudin sun yi yawa sosai, wasu na ganin ba matsala.
     _____________________
Ma'asumiya News Update;
Wakilinmu;
    👇🏻
Mahadi Tukur Almizan

DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post