'Yan bindiga sun fara karbar Haraji wurin mai son noma a gonar sa a jihar Zamfara.


Al’amuran tsaro a Zamfara sun dauki sabon salo bayan da ‘yan bindigar da suka addabi mutanen jihar da kashe-kashe suka kakabawa manoma biyan haraji kafin su noma gonakin su.
.
Mutanen jihar ta Zamfara na cigaba da zama cikin zulumi da tashin hankali bisa halin da ‘yan bindiga, da suka hada da barayin shanu da ‘yan fashi suka jefa rayuwar mutane a ciki.
.
A wata hira da gidan Radiyon Faransa tayi da Bashir Ibrahim Idris, wani mazaunin jihar ta Zamfara, ya bayyana cewar matsalar tsaro a Zamfara na kara tabarbarewa duk da kokarin da gwamnati ke yi na shawo kan al’amarin.

https://maasumiya.blogspot.com/2018/06/rigimar-falasdinu-ba-ta-addini-ko.html

Ko a yayin ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Amurka, ya shaidawa sashen Hausa na Radiyon Amurka cewar, an kashe mutane a jihar Zamfara fiye da wadanda aka kashe a jihohin Benuwe da Taraba dake fama da rikicin makiyaya da manoma.
.
Batun biyan ‘yan bindiga haraji kafin mutum ya noma gonar sa dai ya saka mazauna kauyuka cikin fargaba da tashin hankali ganin cewar mazauna kauyukan sun dogara ne kacokan a kan noma da kiwo.
.

Kawo yanzu dai bamu samu bayanai daga bakin hukumomin tsaro da na jihar Zamfara a kan wannan batu ba.


Ma'asumiya Nigeria news updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post