MICECE SOYAYYA??




🌎MA'ASUMIYYA NIGERIAN NEWS UPDATE

Daga wakilinmu zaidu sulaiman shi'a


Wannan tambaya an dade ana kaiwa da kawowa a kanta, masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce tanKamar haka.

Soyayya ita ce nuna kauna daga bangarori biyu na masu kaunar juna!

Muhammad Hashimu

ya bayyana cewa! Soyayya ita ce ni'ima mafi daukaka da Allah Ya ba wa bayinsa, Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun kule su cure' sukuma game cikin zuciya daya, Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki daya. Soyayya ita ce mutum biyu cikin mutum daya, Abin da ake nufi a nan shi ne. idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai shi. ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato kenan sun zama mutum daya cikin jiki biyu.

Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu ce mun bayyana hakikanin ma’anar soyayya ba, Domin ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba, Sai mutum ya shige ta sannan zai san ta.

KASHE-KASHEN SOYAYYA.


Soyayya ta kasu zuwa gida uku kamar haka!

(1) Soyayya Don Sha’awa.
(2) Soyayya Don Abin Duniya.
(3) Soyayya Ta Hakika Ko Gaskiya.

SOYAYYA DON SHA’AWA

A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace,bsai daya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin dayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa. ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu.To irin wannan abun' soyayya bace sha’awa ce da zarar daya daga ciki ya biya bukatar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.

(2) SOYAYYA DON ABUN DUNIYA


Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kudi, ko dan kyau ko dan wani kyale-kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba ne, da zarar abun da ake yin soyayyar don shi ya gushe. sai a fara shirye-shiryen nesantar  juna.

(3) SOYAYYA TA HAKIKA KO GASKIYA

Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tunani wajen kafa ta, Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha'awa ko wani abun duniya ba. ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya itace ta gaskiya. Kuma ita ce irin soyayyar da take dorewa wadda ba ta yankewa har abada.



~sahannu~

Barrister Nuraddeen isma'eel

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post