KASHE-KASHEN NAJASA.




Daga shafin Ma'asumiya Nigerian News Updates, A cikin darasin  mu na AHKAMUL ISLAM fitowa ta (4)


"Kamar yadda muka saba kawo muku darussa Akan Ahkam yauma gamu munsake  dawowa Acikin wannan fili inda zamuyi magana akan NAJASA dani MUDASIR BARA'A MALUNFASHI zan Gabatar muku.

Da farko

i) GIYA:- GIYA najasa ce. haka nan kuma duk wani abu mai sa maye idan ya kasance ahi a kan kansa ruwa ne  ma'ana ba wai an jika shi bane ko kuma an narkar da shi ne.

j) FIKA:- WAni abin sha ne mai sa maye wanda ake samu daga alkama bisa umurnin likita(ruwan alkama)shi mai tsarki ne

K) gumin rakumi mai cin bahayan dan Adam:- wanda yake cin bahaya na dan adam guminsa najasa ne

5. Idan najasa tashiga chikin tukunya yayin tafasar da wani abu shima abun ya najasantu.haka kuma wannan tukunyar kuma da wan nan abun tafasar bazata tsarkake najasar ba haka kuma zafin wutar.

6.ya haramta ci da shan najasa , kamar yadda ya haramta mutum ya sabbaba wa waninsa ci ko shan najasan.

7.idan abu mai tsarki da mai najasa suka hadu kuma ya kasanche dayansu ko dukkansu suna da danshi mai naso.to mai tsarkin shima ya zama najasa.

8.idan aka samu najasantu war wani abu kuma ana shakkun tsarkinsa, ya kasance najasantacce idan kuma ana da sanin tsarkin wani abu kuma Ana shakkun najasantuwar to ya kasance tsarka kakke.

Wassalamu alaikum wara hamatullah

Insha Allah sati mai zuwa zamu tashi A.9 .haramchin najasantar da wani ban gare na ALKUR'ani

~Sa Hannu~ DMS

Amadadin 
editor Nura Isma'eel Baba

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post