AKAN IDONA:-Naga Sheikh Turi sanye da bakar Half-Jumper da bakin wandonta irin Pakistan dinnan, takalminsa Sandal da Safarsa baka.A Lokacin da abubuwa suka rincabe a Gyallesu, Muminai Sunata Shahada, fajirai fasikai Makiya Allah suna ta dada karfi akan raunanan da basa da ko tsinke da sunan makamin kashe makasanmu. 


A wannan gabar suka harbeni, ta gaban Sheikh aka wuce dani yana ta "Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil, wannan kuskuren ba za'ai damuba, Yan Uwa mu tunkaresu", baifi minti 15 ba da ajiyeni a inda ake ajiye Shahidai  da marassa lafiya, wadda cikarmu yasa ba inda yanzu za'a ajiye gawa ko marassa lafiya, a wannan gabar suka budewa Sheikh Turi wuta suna cewa "He's Turi shoot him", bayan an daukosu zuwa cikin Yan Uwa, suka biyomu har gidan Jagora da sauran sassan inda ake ajiye 'Casualities', suka karisa marassa lafiya suka bankawa gidan wuta. 


Kuma a cikin gidan akwai Sheikh Zakzaky da Iyalansa, da sauran tsuntsayen da yake kiwo, harma da wadda suka hada shekarsu don su ci Arzikin wannan bawan Allahn Muklusi.


Buhari Allah ya'isa.


-Muhd Bala Afuwa.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ya sakawa wadanda aka zalunta' Allah kajiqan shahidai baki daya

    ReplyDelete
Previous Post Next Post