Mu Daku Waye Kirkirar Yahudawa ???



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

                              (ƘALU BALE GAREKU) 


Daga cikin abubuwan da maƙiya Shi'a suke yiwa Ƴan Shi'a sharri da ƙage dashi , shine danganta Shi'anci da yahudanci , wai asalin Shi'a wani Bayahude da ake kira Abdullahi ɗan Saba'i ne ya ƙirƙirota , abun dariya da takaici !!! 

Tare da cewa har manyan Malamansu sun ƙaryata wannan maganasuka tabbatar da bata da asali , suka tabbatar da ba komai bace face yarfe da kuce dan a ɓata Shi'a da Shi'anci , Bugu da ƙari akan haka ga wani ƙalu bale ga duk wani mai tuhumar Asalin Aƙidar Shi'a da Yahudanci :


In har kun kasance masu gaskiya cikin abunda kuke faɗa , ga littattafan Shi'a nan sun cika Duniya tun daga ƙarni na farko har zuwa yau , in kun isa ku kawo mana ruwaya ko da guda ɗaya ce da aka ce wannan Abdullahi ɗan Saba'i ne ya rawaito ta (Ba an tawaito akansa ba ) , ko ku kawo mana wata Aƙida guda ɗaya daga cikin Aƙidun Shi'a da aka ruwaito cewa daga Abdullahi ɗan Saba'i take , ko ku kawo mana wani hukuncin Fiqhun Shi'a guɗa daya tak da aka ce ɗan Saba'i ne ya rawaito shi ko daga gareshi yake .

Don Allah da Annabi mun ƙalu balance ku kuyi hakan Ya ku tarin .....


BUGU DA ƘARI 


Amma ku kuma babu wani littafin Tafsiri naku da za'a buɗe face an samu riwayar Addinin ku daga Ka'abul Ahbari , Wanda kowa yasan tsohon ƙasurgumin malamin Yahudawa ne wanda ya musulunta a Zamanin Mulkin Umar Bin Khaɗɗab, daga nan ya zama Babban Maruwaicin Hadisi da kuke ji da shi a Addinin ku , abune tabbatacce Ka'abu ya ƙware wajen rawaito ruwayoyin tastuniyoyi na Isra'iliyyat , kuma yana da Tafsiri a Addinin ku saɓanin mu , sam Abdullahi bin Saba'i bai da wani tasiri a wurinmu , sai dai ruwayoyi da suke la'antar shi in ma akwaishi ɗin yana samuwa kenan fa ! 


Gini akan yadda kuke riyawa Mu da ku waye ƙasurgumin Bayahude yayiwa Tasiri a Addinin sa ?


Waye yake cewa Bayahude : Radiyallahu anhu a litattafan Tafsirin sa in ba ku ba ?


Waye yake la'antar Bayahude a littattafansa in bamu ba ?


Su waye suka ce Bayahude ne Malamin Sahabbai a fannin Tafsirin Alkur'ani in ba ku ba ?


Ba Ka'abul Ahbari ba , akwai manyan manyan malaman Yahudawa da suka shahara suka yiwa Musulunci kuste kuma suka wayi gari sune manyan turakunku na Addini , Kamar su Abdullahi ɗan Salami da Wahbu ɗan Maniyyata da sauransu ....

Kai manyan waɗanda kuke ji dasu a hadisi malamanku sun tabbatar da daga wajen Yahudawan suke rawaito Hadisai kuma an ingantasu kuna Addini da su .


Mhm !!! Wai mai gidan gilashi ne yake cewa ayi wasan jifa da dutse !!!


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post