Lebanon ta fuskanci mummunar rana sakamakon hare-haren Isra'ila kan Hezbollah
Sama da mutum 270 aka kashe yayin da 1,000 suka jikkata sakamakon hare-haren bama-baman Isra'ila a Lebanon, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta sanar.
Wannan na zuwa bayan Isra'ila ta yi gargadin cewa za ta ƙarfafa hare-hare kan Hezbollah.
Dubban mutane ne suka tsere daga gidajensu bayan da rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare wurare 800 na maɓuyar Hezbolla tare da gargaɗi ga fararen hula.
Hezbollah ta ƙaddamar da hare-haren rokoki a arewacin Isra'ila bayan hare-haren. Amma jami'an lafiyar Isra'ila sun ce mutum ɗaya kawai ya ji rauni.
Rana ce mai muni kusan cikin shekara a faɗan kan iyaka da ke ƙara haifar da barazanar yaƙi.
Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya ce yana tsoron rikicin zai iya mayar da Lebanon "wata Gaza."
Watanni sha ɗaya na faɗa tsakanin Hezbolla da Isra'ila wanda yaƙin Gaza ya haddasa ya kashe ɗaruruwan mutane, galibinsu mayakan Hezbollah, tare da raba dubban da muhallinsu musamman a yankunan kan iyakokin ɓangarorin biyu.
Hezbollah ta ce tana faɗa ne domin goyon baya ga ƙungiyar Hamas ta Falasdinawa, kuma ta ce ba za ta daina ba har sai an tsagaita wuta.
Dukkanin ƙungiyoyin biyu sun samun goyon bayan Iran waɗanda Isra'ila da Birtaniya da sauran ƙasashe suka ayyana a matsayin ƴanta'adda.
Kafofin yada labaran Lebanon sun ruwaito cewa jiragen yaƙin Isra'ila suka fara kai jerin hare-hare a ƙasar da safiyar Litinin.
Sun kai hare-hare a wurare da dama a kudancin Sidon da Marjayoun da Nabatieh da Bint Jbeil da Tyre da Jezzine da Zahrani, da kuma wasu sassa na lardin Bekaa mai tsaunika, kamar yadda kamfanin dillacin labaran NNA ya bayyana.
Daga baya, kafar ta ce hare-haren Isra'ila sun yi ƙamari da sassan kudanci da kuma Bekaa, wanda suka yi ta'adi sosai.
Ministan lafiya na Lebanon Firas Abiad a ranar Litinin ya ce mutum 274 aka kashe a hare-haren, yayin da mutum 1,024 suka jikkata.
Sai dai bai bayyana adadin fararen hula ba ko kuma mayaƙan da aka kashe amma ya ce 21 daga ciki yara ne, 31 kuma mata.
Ya ƙara da ce dubban mutane ne aka raba da gidajensu sakamakon hare-haren.
@Ma'asumah Nigerian News update